Garkuwa da mutum: An saki Sheikh Al-garkawi bayan kwana uku da sace shi

Sheikh Ahmad Al-garkawi

Mai magana da yawun rundunar yace jami'an rundunar sunyi nasara kubutar da malamin ranar lahadi 5 ga watan Agusta ba tare da biyan kudin fansa.

Labari ya bayyana cewa shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Al-garkawi wanda masu garkuwa da mutane suka sace ya koma ga iyalen.

Malamin yua koma gida bayan kwanan uku a hannun barayin.

A rahoton da jaridar Premium times ta fitar, kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna Mukhtar Aliyu ya tabbatar da sakin malamin.

Mai magana da yawun rundunar yace jami'an rundunar sunyi nasara kubutar da malamin ranar lahadi 5 ga watan Agusta ba tare da biyan kudin fansa.

Ya kara da cewa suna bincike kan wasu mutane biyu da aka kama da zargin sa hannunj su wajen sace shehin malamin.

Barayin dai sun sace malamin ne a yammacin ranar alhamis a gonar shi dake wajen garin Kaduna tare da wasu daliban sa su uku.

Sai dai yan sanda basu yi karin haske game da daliban sa da aka sace tare dashi.

Source: Pluse ng

Sharing is caring!

You may also like

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *